Da Ɗumi Ɗuminsa! Amurka Ta Yi Gargadi Kan Yiwuwar Kai Hari A Babban Birnin Tarayya Abuja Nigeria

Alfijr ta rawaito Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya ce ana fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci a Najeriya, musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Alfijr Labarai

A cikin sanarwar tsaro da aka ba wa ‘yan kasarta, Ofishin Jakadancin Amurka ya ce harin na iya hadawa da, gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan kantuna, otal-otal, mashaya, gidajen cin abinci, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin sufuri, amma ba a iyakance wuraren da ake zaton kai harin ba.

Ofishin Jakadancin Amurka zai ba da rangwamen ayyuka har sai an samu sanarwa,” in ji ofishin jakadancin Amurka.

Ofishin jakadancin Amurka, ya shawarci ‘yan kasar da su guji duk wani tafiye-tafiye ko motsi maras muhimmanci, su kasance a faɗake, kaurace wa taron jama’a da sake duba tsare-tsaren tsaronsu da kuma ci gaba da cajin wayar salularsu a cikin gaggawa, gami da ɗauke da shaidar da ta dace.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Solacebase

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *