Da Ɗumi Ɗuminsa! Dan Ganduje Ya Yunkura Wajen Gurfanar Da Mahaifinsa A Kotu Kan Kudi N190m

Alfijr

Alfijr ta rawaito, babban dan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Abdulazeez Ganduje, yana shirin gurfanar da gwamnatin mahaifinsa a gaban kotu bisa rashin biyan kamfaninsa na Global Firm Nigeria Limited zunzurutun kudi har naira miliyan 82 bayan ya kammala kwangilar.

Alfijr

Rahotanni sun ce, a ranar 13 ga Fabrairu, 2020, Gwamna Ganduje ya amince da bawa kamfanin dansa kwangila kan kudi N189,913,590.54.

A ranar 7 ga Mayu, 2021, an biya kamfanin Naira 94,556,795.27 ta Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jiha, kashi 50 na kudin kwangilar.

Alfijr

Wani bincike ya bayyana cewa kin amincewa da biyan bashin da gwamnan ya yi ba zai rasa nasaba da koken da Abdulazeez ya kai ga hukumar EFCC a watan Satumbar 2021 kan mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, a kan wasu makudan kudade na miliyoyin naira da shi (Abdulaziz) ya jagoranta.

A wata wasika da ya aikewa ma’aikatar ilimi, lauyoyin Abdulazeez sun bukaci a biya su N82,662,464.04 cikin kwanaki bakwai ko kuma a dauki matakin shari’a.

Mun tattaro wannan bayanan ne a Jaridar Daily Nigeria

Slide Up
x