NAFDAC ta kama Gurbataciyar Ganda Ta Miliyan 23

Alfijr

Alfijr ta rawaito, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta kama tan 120 na ganda mai ɗauke da sinadarai wadda aka shiga da ita ƙasar.

Alfijr

BBC ta bayyana hukumar ta fitar a shafinta na Twitter ranar Lahadi, ta bayyana kamun gandar a wurare shida a garin Lagos

Farfesa Majosola Adeyeye itace Shugabar hukumar ta NAFDAC, ta bayyana cewa mutum bakwai da ake zargi da wannan lamarin ana gudanar da bincike a kansu.

Alfijr

Majosola ta kara da cewa tuni aka ɗauki samfarin gandar domin kai ta ɗakin gwaji domin gano ingancin ta don gudun cutar da al umma.

Ta kuma bayyana cewa an yi ƙiyasin farashin gandar kan kusan naira miliyan 23m