Sarauniyar Ingila Ta Kamu Da Cutar korona

Alfijr

Alfijr ta rawaito fadar Buckingham ta bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.

Alfijr

Sanarwar ta cigaba da cewar, za a ci gaba da duba lafiyarta da duka hanyoyin da suka dace, don cigaba da samun lafiyarta

Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta haɗu da babban ɗanta kuma magajinta wato Yarima Charles wanda shi ma ya kamu da korona a makon da ya gabata.

Alfijr

BBC ta bayyana sanarwar na zuwa ne mako guda bayan da sarauniyar ta kafa tarihi ta zama wadda ta fi daɗewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ingila bayan ta cika shekara 70 a kan mulki a ranar 6 ga watan Fabrairu