Kungiyar Arewa Ta Bukaci A Kori Manyan Jami’an NNPC, Nan Da Sa’o’i 72

Alfijr

Alfijr ta rawaito gamayyar kungiyar Concerned Northern Forum ta mika wa Gwamnatin Tarayya wa’adin sa’o’i 72 na korar dukkan ma’aikatan kamfanin man fetur na Najeriya saboda karancin man fetur da ake fama da shi a fadin kasar nan.

Alfijr

Sanarwar da shugaban kungiyar Ibrahim Bature da Abdulsalam Kazeem suka sanya wa hannu a ranar Lahadi a Kaduna.

Sun kuma bukaci Manajan Daraktan Rukunin NNPC, Mele Kyar, da babban jami’in hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya Midstream and Downstream, Farouk Ahmed, da su yi murabus nan take.

Alfijr

Kungiyar ta yi gargadin cewa gazawar gwamnati ta biya musu bukatunsu, zai tilasta musu daukar matakin gaggawa.

Kungiyar ta ci gaba da cewa, “Kamfanin NNPC tare da masu shigo da man fetur ba tare da sun sani ba, wadanda ba su da lasisi ko kuma hukumomin da abin ya shafa da ke da alaka da shigo da man fetur suna jawo mu koma baya saboda kura-kuran da suka yi da gangan.

Alfijr

Kungiyar ta kara da cewa a madadin al’ummar yankinmu muna bukatar wadannan abubuwa cikin sa’o’i 72;

Gano duk magidanta da ke da irin waɗannan abubuwan da aka ambata da kuma isassun diyya da aka biya su don lalacewar motocinsu, injuna da kayan aikinsu a yankinmu.

Alfijr

Suka kara da cewar, ya kamata GMD na NNPC, Mallam Mele Kolo Kyari, da Engr. Farouk Ahmed, babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (Nigeria Midstream and Downstream), su mika takardar murabus din nasu ba tare da bata lokaci ba, saboda karya tarihin gwamnati mai ci kan matsalar karancin mai;

Sannan kuma a kori dukkan ma’aikatan kamfanin na NNPC ba tare da biyan diyya ba.

Alfijr

Suka kara da fadin, ya kamata mahukuntan NNPC su fito da sahihin sunayen wadanda ke da hannu a cikin wannan badakala da abin kunya na kasa; “Ko kuma idan ba a biya mu bukatunmu nan da kwanaki uku masu zuwa ba, za mu mamaye dukkan ofisoshin shiyya-shiyya na NNPC da kuma rassanta a fadin yankin mu da babban birnin tarayya Abuja.

Sun kuma tabbatar wa da mahukunta cewar, wannan ba barazana ba ce kawai.

Alfijr

Za mu bi diddigin cikakken mataki bayan cikar wa’adin da aka ba mu, kuma hakan zai zama babban gwaji a bangaren gwamnati kan yaki da cin hanci da rashawa da rashin da’a.

Slide Up
x