Dakarun Sojojin Nigeria Da Hadin Gwiwar Civilian JTF Sun Sami Gagarumar Nasara Kan BHT/ISWAP

Alfijr

Alfijr ta rawaito dakarun Sojojin Nigeria Bataliya ta Task Force 149 tare da hadin gwiwar Civilian JTF a wani sumame da sukayi yayin da suke sintiri a ranar Alhamis 10 ga Fabrairu, sun sami wata gagarumar nasarar fatattakar ‘yan ta’addar BHT/ISWAP da dama a kauyen Dunga Lawanti da ke kusa da Gubio a jihar Borno.

Alfijr

A wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na Facebook, Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, babura biyu da dai sauransu.

Alfijr

Har yanzu ana ci gaba da sintiri a yankin gaba daya.