Alfijr
Alfijr ta rawaito, rundunar ‘yan sandan Brazil ta kama wani mutum da suka tabbatar da cewa ya yi kutse cikin asusun bankin Neymar tare da satar wasu kananan kudade da suka kai sama da dala 40,000, in ji jami’ai a Sao Paulo.
Alfijr
‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya yi kutse ne a wani banki da ba a bayyana sunansa ba inda dan wasan Paris St-Germain (PSG) da Brazil da mahaifinsa manajan kasuwancinsa ke da asusu.
An kama matashin mai shekaru 20 a ranar Laraba “saboda damfarar abokan huldar banki”, in ji sanarwar.
Alfijr
Ko da yake rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan dan wasan ba a cikin sanarwar, amma jami’in da ke kula da lamarin ya ce Neymar ne.
Ya bayyana yadda ake zargin satar da aka yi a gidan talabijin na Brazil Brasil Urgente. “Me wannan yaron ya yi” in ji Fabio Pinheiro Lopes.
Alfijr
Mutanen sun lura da yadda matashin ya yi canjin kudi kimanin 10,000 reais ya sake yin na dala 1,912.59, sannan 10,000, sai 20,000, sannan 50,0000 kuma jimillar ta kai 200,000.”
Lopes ya ce asusun da abin ya shafa na Neymar ne kuma mai yiwuwa mahaifinsa ne ke kula da kudaden.
Alfijr
Lokacin da suka gano sai suka kira bankin. Bankin ya biya wanda aka yiwa satar, tare da bincikar wanda ke da hannu a ciki.” Inji shi.
Jami’in yada labarai na Neymar bai ce komai ba game da lamarin lokacin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tuntubi shi.