Dubun Wasu Yan Damfara Ta Cika A Kano! EFCC

Alfijr ta rawaito hukumar EFCC ta kama wasu mutane biyu da laifin zamba a jihar Kano

Alfijr Labarai

Hukumar EFCC reshen jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Gazali Ado, mai shekaru 35 da haihuwa wanda ya bayyana a matsayin ma’aikacin hukumar EFCC a Manhajar Google.

An kama shi ne biyo bayan wani koke da wani Kenneth Nwarize ya shigar inda ya yi zargin cewa wanda ake zargin ya damfare shi kudi N150,000 (Naira Dubu Dari da Hamsin Kadai) bisa zargin cewa shi ma’aikacin Hukumar EFCC ne.