Alfijr ta rawaito Hukumar kashe gobara ta Jihar Lagos ta sanar da samun raunuka wani mutum a ranar Litinin, bayan da wani abu ya fashe a wani gidan Mai, mai zaman kansa da ke garin Badagry na jihar.
Alfijr Labarai
Abel HusuBabban jami’i nr da ke kula da reashen hukumar ta Badagry, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) faruwar lamarin
Ya kara da cewa hukumar tasu ta sami labarin faruwar ne a gidan man Yemoral Oil and Gas Petrol Station da ke kan hanyar Ajara a Badagry da misalin karfe 8:55 na ranar ta Litinin.
Inda jami’anmu suka isa gidan man bayan minti 10 da sami rahoton, kuma nan take suka fara kokarin kashe wutar
Husu yace, binciken da muka gudanar ya tabbatar cewa wani direban mota ne ya Haddasa faruwar gobarar, bayan da ya riga ya sayi man fetur a cikin motarsa
Alfijr Labarai
Bayan da mai motar ya tayar da injin motar sai ta yi bindiga, inda gobara ta tashi nan take, a cewar sa
A nasu bangaren ma’aikata a gidan man sun shaida wa NAN cewa wani mutum ne ya yi sanadin gobarar bayan da ya amsa wayarsa a daidai lokacin da ake zuba ma sa fetur cikin wata jarka.