Alfijr Labarai
Alfijr ta rawaito dubun wasu yan fashi da adaidaita sahu ta cika a daren Juma a da misalin karfe 10 na dare
Alfijr Labarai
Wata majiya da ta tattauna da alfijr ta tabbatar cewar yan fashin sun tare wasu mutane ne inda suka yi musu fashin wayoyinsu kuma suka gudu a nan titin sharada daf da gidan Man A A Rano.
An sami nasarar cimma yan fashin adaidaita sahun ne daidai makabartar Tukuntawa dag bakin titi da taimakon wani mai mota daya kare su
Kokarinsu na tsere wa har suka bugawa wani bawan Allah dan Buda a kirji, yanzu haka an kaishi asibiti da taimakon yan sandan sharada.
Alfijr Labarai
Da taimakon Allah mutane suka yi musu tara tara aka sa kamasu su biyu, nan take kuma aka kone babur din adaidaita din su kuma sunan rai a hanun Allah bayan da jama a suka ragargazasu kafin a tafi dasu ofishin yan sanda sharada.
Sauran bayani zasu zo idan muka sami ji daga bakin kakakin yan sandan kano
Ga Video nan