Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Sake Korar Jami inta Bisa Samunsa Da Laifin Cin Zarafi, Rashin Da’a

Alfijr Labarai

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori Kofur Opeyemi Kadiri bisa samunsa da laifin cin zarafi, rashin da’a

Alfijr ta rawaito rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori Jami inta Kofur Opeyemi Kadiri mai lamba 509745 da ke aiki a hedikwatar Dolphin Dibisional, na rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, bisa samunsa da laifin cin zarafi, rashin bin doka da oda, da kuma cin zarafin wani mutum.

Alfijr Labarai

An kama Kofur Opeyemi Kadiri a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta a ranar 3 ga Agusta, 2022, yana cin zarafin wani farar hula.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (FPRO), CSP Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a, ya ce jami’in da aka kora, wanda ya shiga aikin rundunar a ranar 6 ga watan Disamba, 2016, an kama shi yana binciken wayar wani matafi a gefen hanya sabanin umarnin hukumar. Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya tabbatar da haka.

Alfijr Labarai

“Hakazalika ya ci zarafin matafiyin da ya yi yunkurin kawo masa odar.

Korar tasa ta fara aiki ne daga yau 12 ga watan Agusta, 2022.

“Rundunar ‘yan sanda ta na yin kira ga jami’an rundunar da su kiyaye da kwarewa da wayewa ga jama’a wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada.

“Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su tabbatar da gudanar da ayyukan da suka dace a duk wata ganawa da jami’an ‘yan sanda don kauce wa cin zarafi da za a iya gurfanar da su,”

Slide Up
x