EFCC Ta Mayarwa Hukumar Inshorar Lafiya (NHIS) Naira biliyan 1.5 Da Aka Damfareta.

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta maido wa NHIS Naira biliyan 1.5 a ranar Juma a 18th February 2022

Alfijr

EFCC, ta rawaito haka ne a shafinta na sada zumunta a yau Juma, hukumar yace a ranar 10 ga watan Fabrairun 2022 ta mayar da kudaden da suka kai N1, 550,000.000 (Naira biliyan daya da miliyan dari biyar da hamsin) ga tsarin inshorar lafiya na kasa, NHIS.

Asusun na daga cikin kudaden da wasu bankunan kasuwanci suka yi damfara tare da kin aikawa da su zuwa asusun ajiyar su na Treasury Single Account, TSA, tun a shekarar 2015.

Alfijr

Tun a ranar 16 ga Satumba, 2021 Hukumar ta saki N1, 300,000,000, da aka kwato daga bankunan zuwa ga Hukumar.

Slide Up
x