Abubuwan Dake Sanya Wasu Daga Cikin Fulani Aikata Miyagun Laifuka! Inji Kungiyar Miyatti Allah

Alfijr

Alfijr ta rawaito, kungiyar Fulani ta ‘kasa miyatti Allah Kautal-Hore tace tsagwaron rashin adalci da wariyar da ake nuna Fulani ya sanya wasu daga cikinsu aikata miyagun laifukan da ake zarginsu da yi a sassan kasar nan.

Alfijr

Shugaban ‘kungiyar na kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Dutsen jihar Jigawa.

Badejo ya kara da cewar, ayyukan garkuwa da mutane don nemar kudin fansa, na daga cikin muggan ayyukan da ake zargin fulani da aikatawa sakamakon matsesu da nuna banbanci da gwamnatocin arewa ke nuna musu tun da dadewa.

Alfijr

Ya kara da cewa hatta tsangwamar da gwamnatocin kudancin kasar nan ke nunawa fulani, na faruwa ne sakamakon kin jansu a jika da yi musu a arewacin kasar, mai makon kula da rayuwarsu ma sai amfani dasu don cimma manufar siyasa.

Bisa hakanne ma ya bukaci mahukunta su sauya tinani kan yadda suka dauki fulani ta hanyar samar musu da makarantun ilimin zamani dana addini, domin fahimtar rayuwa, sai kuma samawa makiyayan guraran zama dana kiwo na dindin, kamar yadda akewa sauran al’umma ayyukan ci gaban rayuwa, wadda yace tini gwamnatin jihar Jigawa ta fara aiwatarwa a cewarsa.

Slide Up
x