Farfesa Adamu Gwarzo Ya Kira Ga Daliban Kimiyyar Gwaje-gwaje Da Su Koyi Ilimin Harsuna Mabambanta

Alfijr

Alfijr ta rawaito shugaban kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci daliban Jami’ar da ke karatun kimiyyar gwaje-gwaje da su koyi ilimin harsuna da dama domin samun damar cin gajiyar ayyukan yi da ake da su a fadin duniya baki daya.

Farfesa Gwarzo ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rantsuwar daliban kimiyyar dakin gwaje-gwajen karo na 7 wanda kungiyar likitocin gwaje-gwaje ta Nijeriya wato ‘The Medical Laboratory Science Council of Nigeria’ a turance ta gudanar a birnin Tarayya Abuja.

Cikin dalibai 383 da aka yaye daga Jami’o’i daban-daban a fadin duniya, Jami’ar Maryam Abacha American University, dake Maradi ta kwashi kashi 50 cikin 100 cikin wadanda aka rantsar da su a kungiyar.

Alfijr

Farfesa Gwarzo wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya kuma jaddada bukatar su na kasancewa jakadu nagari ga Jami’o’insu da ma kasar baki daya a duk inda suka samu kansu.

A yayin da yake yabawa jajircewa da kuma adalcin shugabancin kungiyar likitocin dakin aikin gwaje-gwaje ta Nijeriya kan kwarewarsu, Farfesan ya kuma godewa gwamnatin Tarayya bisa samar da yanayi mai kyau.

Alfijr

A cikin jawabinsa, Magatakardar Kungiyar, Dakta Toman Erhabor ya bayyana Kimiyyar gwaje-gwaje a matsayin wata kwararriyar fasaha mai tasirin gaske da aka tsara domin samar da babban tushe na ilimin kimiyya da kuma amfani da shi a cikin tsarin kiwon lafiya.

Erhabor ya bayyana cewa rantsuwar zai bai wa daliban da suka kammala karatun digirinsu a bangaren kimiyyar gwaje-gwaje dama a cikin aikace-aikacen da suka da hada da fannin likitanci, masana’antar harhada magunguna, cibiyoyin bincike, masana’antar abinci da kuma kayan bincike da kera injina.

Alfijr

Ya kuma bukaci kungiyar da ta dauki nauyin daukar dalibai ‘yan kasashen waje dari uku da tamanin da uku tare da yin kira a gare su da su ci gaba da nuna kwarewa wajen bunkasa bangaren.

Shugaban kungiyar ya yabawa Jami’ar Maryam Abacha American University, Maradi bisa yadda take nuna kwazo a bangare ilimi tare da yin kira ga sauran Jami’o’in Afirka masu zaman kansu da su yi koyi da Jami’ar domin bunkasa ilimi.