Shakka Babu! Kutumbawa Sune Tushen Arziki Da Cigaban Kano. Inji Farfesa Abdallah

Alfijr

Alfijr ta rawaito Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce Kutunbawa su ne tushen arzikin Kano, saboda sai da suka shuka suka kafa sannan wasu suka zo suka girba, idan da ba su yi ba babu wanda zai yi.

Farfesan ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na zuriyar Kutunbawa da suke gabatarwa a duk shekara don karin zumuncin juna, wanda wannan karon taron ya gudana a makarantar Rumfa College da ke birnin Kano.

Ya cigaba da cewa idan da ba su yi ba babu wanda zai yi, idan da sun lalatar da abin da ba za ka ji a na yi wa Kano kirari da Ko da me ka zo an fika ba, kuma tun lokacin Abagayawa Kano ta ke da wannan arzikin a cikinta.

Alfijr

Farfesan ya kara da cewar Kutunbawa da Fulani duk abu ɗaya ne kada mu yadda a kawo mana rabe-rabe ko wata fitina, abinda zai ɗaukaka a wajen Ubangiji ba kutunbacinka ba ne ba Fulatancinka ba ne imaninka ne, domin shi ya kamata ya zame maka jagora domin haka babu abinda zai hana mu haɓaka al’adunmu.

Farfesa ya bada shawarar ga Kutunbawa da a samu wata rana da za a dinga yin bikin tunawa haihuwar Sarki Alwali a duk shekara ya zama ranar Alwaliy.

Alfijr

A nasa bangaren Farfesa Tijjani Muhammad Naniya masanin tarihi da ke Jami ar Bayero ta Kano ya ce sarakunan Kutumbawa su ne suka bada cikakkiyar gudunmawar da Bahaushe ya zama abinda ya zama a kasar Hausa, dole mu girmamasu sannan mu yi masu addu’a ta musamman.

“Domin da ba don gudummawar da suka bayar ba; to da ina Kanon take? Kano ai ta samu ne domin ƙoƙarin da suka yi da ba su yi ba ina Kanon ta ke?

Alfijr

Farfesa Naniya ya bada amsa da cewa ba kowa, ai ba ma za a zauna ba saboda duk wanda ya zauna za a zo a yaƙe shi, Kutumbawa ne suka zauna suka bai wa Kano asali suka bai wa Kano mazauni suka bai wa Kano tsaro wannan Badala da ta kewaye Kano wanda a yanzu ake rusa mana ita asali da daraja da bunƙasar Kano.

Mai Unguwar Kutunbawar Kano Alhaji Mustapha Abubakar ya ce shekara 10 ana wannan taro amma ba a taba yin irin wanda ya kayarar ba irin na wannan shekarar kuma mutane sun amsa kira daga ko ina a fadin kasar nan.

Alfijr

Sannan ya godewa Allah da farfesoshi da Sarakuna da ‘yan jarida da dukkanin ‘yan wannan zuriya mata da maza da suka halarci wanna taron mai din bin tarihi.

Mai Unguwar Kutunbawar ya kuma kara kira da ayi hadin kai tare da zumunci domin Allah, wannan shine zai kara ciyar damu gaba.