Alfijr

Alfijr ta rawaito shugaban kuma wanda ya kafa Jamiāar Maryam Abacha American University da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci daliban Jamiāar da ke karatun kimiyyar gwaje-gwaje da su koyi ilimin harsuna da dama domin samun damar cin gajiyar ayyukan yi da ake da su a fadin duniya baki daya.

Farfesa Gwarzo ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rantsuwar daliban kimiyyar dakin gwaje-gwajen karo na 7 wanda kungiyar likitocin gwaje-gwaje ta Nijeriya wato āThe Medical Laboratory Science Council of Nigeriaā a turance ta gudanar a birnin Tarayya Abuja.
Cikin dalibai 383 da aka yaye daga Jamiāoāi daban-daban a fadin duniya, Jamiāar Maryam Abacha American University, dake Maradi ta kwashi kashi 50 cikin 100 cikin wadanda aka rantsar da su a kungiyar.
Alfijr
Farfesa Gwarzo wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya kuma jaddada bukatar su na kasancewa jakadu nagari ga Jamiāoāinsu da ma kasar baki daya a duk inda suka samu kansu.
A yayin da yake yabawa jajircewa da kuma adalcin shugabancin kungiyar likitocin dakin aikin gwaje-gwaje ta Nijeriya kan kwarewarsu, Farfesan ya kuma godewa gwamnatin Tarayya bisa samar da yanayi mai kyau.
Alfijr
A cikin jawabinsa, Magatakardar Kungiyar, Dakta Toman Erhabor ya bayyana Kimiyyar gwaje-gwaje a matsayin wata kwararriyar fasaha mai tasirin gaske da aka tsara domin samar da babban tushe na ilimin kimiyya da kuma amfani da shi a cikin tsarin kiwon lafiya.
Erhabor ya bayyana cewa rantsuwar zai bai wa daliban da suka kammala karatun digirinsu a bangaren kimiyyar gwaje-gwaje dama a cikin aikace-aikacen da suka da hada da fannin likitanci, masana’antar harhada magunguna, cibiyoyin bincike, masana’antar abinci da kuma kayan bincike da kera injina.
Alfijr
Ya kuma bukaci kungiyar da ta dauki nauyin daukar dalibai āyan kasashen waje dari uku da tamanin da uku tare da yin kira a gare su da su ci gaba da nuna kwarewa wajen bunkasa bangaren.
Shugaban kungiyar ya yabawa Jamiāar Maryam Abacha American University, Maradi bisa yadda take nuna kwazo a bangare ilimi tare da yin kira ga sauran Jamiāoāin Afirka masu zaman kansu da su yi koyi da Jamiāar domin bunkasa ilimi.