Daga Aminu Bala Madobi
Ana fargabar barkewar karancin man fetur a jihar Kano, bayan da wasu gidajen sayar da mai (filling stations) a sassa daban-daban na birnin suka rufe harkokinsu, yayin da waɗanda ke sayarwa suka ƙara farashin zuwa sama da naira 1,000 a kowace lita.
Rahotonni sun nuna cewa kaɗan ne daga gidajen man ke sayarwa, inda farashin ya kai tsakanin naira 1,050 zuwa naira 1,084 a kowacce lita. Wannan kuwa ya nuna ƙaruwa mai yawa idan aka kwatanta da tsohon farashin kusan naira 900 a kowace lita.
A gidan man NNPC Retail Limited da ke kan titin Murtala Muhammed Way, an nuna farashin man fetur a naira 1,084 a kowacce lita, sai dai a lokacin hada wannan rahoto ba a sayar da man. A daya bangaren kuma, gidan mai na Fara Fara da ke kan titin Hadejia yana sayar da man a farashin naira 1,060 a kowace lita.
Hakazalika, gidan mai na Aliko Oil da ke kan titin Independent Road yana sayar da man a naira 1,060, yayin da IMG Filling Station ke sayar da shi a naira 1,050 a kowace lita.
Wannan lamari ya janyo damuwa a tsakanin direbobi da masu sana’ar sufuri, musamman masu tuka adaidaita sahu, inda suka nuna cewa karin farashin zai yi matuƙar shafar kuɗaɗen shigar da suke samu a kullum.
Wasu direbobin adaidaita sahu damuka tattauna dasu sun tabbatar dacewa tashin farashin zai tilasta musu ƙara kuɗin mota idan har lamarin ya ci gaba, domin su ne ke sayen mai a kullum.
Wani mai mota mai zaman kansa, Ali wagili, ya ce direbobi ba su da wani zaɓi face sayen mai a duk farashin da suka samu. Ya kuma yi gargaɗin cewa idan lamarin ya ɗaure, mutane na iya fara sayen mai da yawa domin adanawa.
Wasu mazauna birnin na ganin cewa wannan matsala na iya kasancewa da alaƙa da tashin hankalin da ke ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin da ya shafi Iran, Amurka da kuma Israel, wanda masana ke cewa zai iya shafar samar da mai da kuma farashinsa a duniya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t