Gobara Ta Ƙone Shaguna A Kasuwar Hajj Camp Da Ke Birnin Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito gobara ta ƙone shaguna huɗu a kasuwar da ke sansanin alhazai ta Kano wato Hajj Camp.

Wasu ganau sun bayyana gobarar ta tashi ne a daren Jumu’a lokacin buɗa baki, a ɓangaren masu sayar da kayan gwanjo, (Gumama).

Shugaban kasuwar Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi ya tabbatar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai kan faruwar lamarin.

Alfijr

Ya bayyana Cewar, wutar ta tashi ne bayan an sha ruwa, ta ƙone shaguna huɗu, an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira, zamu kuma tantance adadin asarar da aka yi, mun kira ƴan kwana-kwana da jami’an tsaro, kuma duka sun bamu gudunmuwa har aka kashe gobarar, ya jajantawa ƴan kasuwar da lamarin ya shafa.

Hajiya Aisha Abduljalal na cikin waɗanda shagunansu ya ƙone ƙurmus ta shaida wa Freedom Radio yadda labarin ya risketa.

Alfijr

“Ina gida ina shan ruwa aka min waya cewa shagona ya kama da wuta, na hawo babur na zo, sai na tarar babu abin da zan ɗauka, jiya na zuba kaya, yau ma na ƙara zubawa saboda fatan cinikin sallah, sai ga wannan tsautsayi” a cewarta.

Ta ƙara da cewa “A hakanmu babu abin da zance sai godiyar ubangiji, aƙalla kayan da suke cikin shagona sun kai miliyan uku amma ban ɗauki komai ba”. Hajiya Aisha ta ƙarasa maganar cikin shashsheƙar kuka saboda alhini.

Alfijr

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, har ma yace tuni jami’ansu suka kai ɗauki.

Slide Up
x