Musulmi Duniya Za Su Azumci Watan Ramadan Har Sau Biyu A Shekarar 2030

Alfijr

Alfijr ta rawaito wasu masu ilmin taurari sun ce a shekarar 2030 mai zuwa, Musulmin duniya za su yi azumin watan Ramadan har sau biyu.

Masanan sun ce watan Ramadana zai bayyana har sau biyu a cikin shekarar!

Na farko a watan Janairu, na biyu kuma zai bayyana ne a karshen watan Disambar shekarar, yanayin da tun 1997 ba a taba gamuwa da shi ba.

Alfijr

Babban dalilin aukuwar haka shi ne bambancin da ke tsakanin shekarar Musulunci da ake lissaftawa da bayyanar wata, da kuma shekarar nasara wadda aka danganta da kwanakin da duniya ke dauka kafin ta zagaya rana.

Wannan yanayin ya taba aukuwa ne sau daya cikin shekara 30 saboda shekarar Hijira ba ta kai tsawon ta nasara da kwanaki 11 ba, kamar yadda Khaled al-Zaqaq, wani mai nazarin taurari dan kasar Saudiyya ya bayyana a Twitter.

Alfijr

Tsawon shekara guda ta Hijira kwana 354 ne, inda shekarar nasara kuwa ke da kwana 365.

Kamar yadda BBC suka wallafa a shafinsu

Slide Up
x