Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin gyaran titin da ya tashi daga club road zuwa titin airport a karkashin shirinsa na gyara manyan titunan kwaryar birnin Kano.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati zata gyara manyan tituna 17 domin inganta sufuri da habaka tattalin arzikin jihar Kano.
Gwamnan ya kara da cewa, gyaran titunan zasu rage afkuwar hadurra a tituna wanda ke haddasa hasarar rayuka da dukiyoyin al’uma.
Ya bukaci kamfanin da zai gudanar da aikin dasu aiwatar da aiki mai nagarta, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba zata lamunci almindahna ko kuma aiki mara inganci ba.
A jawabinsa shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Yusuf Imam Ogan Boye wanda kuma shi ne mataimakin shugabar kungiyar shugabannin kananan hukumomin cikin kyaryar birnin Kano ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yunkurinsa na kyautata titunan birnin Kano.



RK
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ