Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Mutum 11 Don Su Nazarci Cibiyar Da Zata Kare Afkuwar Iftila I, A Jihar

Alfijr

Alfijr ta rawaito an kaddamar da kwamitin kwararru na mambobi goma sha daya kan horar da ma’aikatan kula da bala’o’i domin horar da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da na kasuwanci da sauran masu ruwa da tsaki a kan barkewar iftila i, a jihar.

A lokacin da yake kaddamar da kwamitin a karamin dakin taro na ma’aikatar, kwamishinan ayyuka na musamman (Dr.) Mukhtar Ishaq Yakasai ya bayyana cewa, kwamitin zai fitar da tsare-tsare kan yadda za a horar da ma’aikata na bangarori daban-daban na kasuwanci da masu zaman kansu kan kariya daga barkewar iftila i, a cikin jihar musamman a wuraren da jama’a ke taruwa kamar tashoshi, kamfanonin gine-gine da sauransu

Mukhtar Ishaq Yakasai ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya amince da kafa cibiyoyin bada horo a babban birnin jihar inda ake horas da wadannan ma’aikata na, kasuwanci da masana’antu kan dabarun magance bala’o’i.

Alfijr

Ya umurci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da ta samar da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Kano da kamfanin Landsafe consultancy Ltd, domin sanya hannu kan kwamitin ya tabbatar da cewa ya bayar da rahoton wucin gadi ga kwamishinoni.

Tun da farko a nasa jawabin, Sakataren Zartaswa na hukumar ba da agajin gaggawa ta Jiha Kwamared Dr. Saleh Aliyu Jili ya ce, kafa kwamitin horar da kwararru kan yadda za a shawo kan iftila i, ya samo asali ne sakamakon gobarar da ta faru a tashar Al-Ihsan a tsakiyar shekarar 2021, inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi tare da jikkata wasu da ba su ji ba ba su gani ba.

Alfijr

Sakamakon haka Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurci hukumar SEMA da ta bullo da hanyoyin dakile sake afkuwar irin haka, wanda SEMA ta hada kai da kwararrun masu kula da iftila i, masu zaman kansu domin tallafa wa hukumar kan wannan aiki.

A nasa bangaren, Manajan Darakta na Landsafe consultancy Ltd, kuma shugaban kwamitin Farfesa Rabi’u Abdussalam Magaji ya yabawa gwamnatin jiha bisa hangen nesa da take da shi na daukar matakan riga-kafi kan duk wani ibtila i, da ya barke a duniya wanda ke cikin tsarin duniya.

Alfijr

Farfesa Rabi’u Abdussalam Magaji ya kuma bayar da tabbacin cewa, kwamitin kwararru za su yi aiki tukuru wajen samar da hanyoyin da za a bi domin dakile ko rage yawan barnar da ke faruwa a jihar.

Wakilan kwamitin sun hada da Abubakar Gambo, Ibrahim Muhammad Kabara, Umar Abdulazeez, Hassan Imam, Auwalu Muhammad, Farfesa Rabi’u Abdussalam Magaji. Sauran sun hada da Dokta Isma’il Tijjani, Auwalu Mu’azu Himma, Daraktan Hukumar kashe gobara, Wakilin FRSC da Salusu Musa Aliyu zai yi aiki a matsayin Sakatare

Alfijr

Kamar yadda Auwal A. Sheshe mataimakin daraktan watsa Labarai na Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, ya fitar a 16/03/2022.

Slide Up
x