Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Kama Kayayyakin Jabu Na Sama Da Miliyan Dari N100m

Alfijr Labarai

Hukumar Kare Kayayyakin ta jihar Kano (Cunsumer Protection Council) ta bayyana cewa ta kwace kayayyakin jabu da marasa inganci na sama da Naira miliyan 100 a cikin watanni uku da suka gabata.

Alfijr Labarai

Shugaban riko na hukumar, Baffa Babba Dan’agundi, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa majalisar ta fara bin doka da oda wanda zai kai ga lalata kayayyakin.

Baffa ya jera wasu kayayyakin da aka kwace da suka hada da gurbatattun takin zamani, fulawa, dabino, shinkafa, spaghetti, madara da kuma semolina.

Watan da ya gabata ne majalisar ta tabbatar da gano takin zamani mai dimbin yawa a wurare biyu a jihar sannan ta kama wata mota tirela mai dauke da man semolina da wa adinsa kare a babbar kasuwa da ke cikin birnin Kano.

Alfijr Labarai

Ya kara da cewa an kama mutane 11, sai dai ya koka da cewa hukuncin da aka tanadar a cikin dokar da aka kafa majalisar ba ta da nauyi da za ta iya kawo cikas, inda ya bukaci a sake duba dokar domin yin abin da ya kamata.

Slide Up
x