Alfijr Labarai
Alfijr ta rawaito Hukumar gudanarwar majalisar ta tabbatar da afkuwar gobarar da ta afku a bangaren majalisar wakilai, amma ta bayyana cewa nan take aka shawo kan lamarin.
Alfijr Labarai
“An samu wata gobara da yammacin Alhamis a daya daga cikin sashen, da ke hawa na 2, daki 227 a majalisar wakilai ta Nijeriya, wanda ake zargin ya faru ne a sakamakon matsalar wutar lantarki da wani ya lura da faruwar lamarin, wanda ke aiki a bangaren magatakarda na majalisar wakilai, wanda ba tare da bata lokaci ba ya sanar da sashin kashe gobara na tarayya da ke a harabar majalisar dokokin kasa,
Daraktan Yada Labarai na majalisar Agada Rawlings a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa an kashe gobarar tare da taimakon ma’aikatan da ke bakin aiki inda nan take suka kutsa cikin ofishin da abin ya shafa tare da tura na’urorin kashe gobara a kasa kafin isowar jami’in kashe gobara.
Saboda haka, hadin gwiwar da aka yi cikin gaggawa, an dakile gobarar ga ofishin da abin ya shafa tare da kashe wutar lantarki a reshe domin samun cikakken bincike kan lamarin.
Alfijr Labarai
“Ana sa ran bayan tantancewar da hukumar kashe gobara da kuma daraktocin ayyuka suka yi, manyan jami’an majalisar wakilai da na ofishin ‘yan majalisar wakilai, za a dawo da su nan take.
“Hukumar gudanarwa ta yaba da kokarin da sashin kashe gobara wajen taimakawa wajen dakile barkewar gobarar”, in ji shi.