Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Wani Yaro Dan Shekara 18 Ya Kashe Wata Mata Da Tabarya A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama yaron dan shekara 18, da ake zargi da kisan wata mata dake unguwar Danbare ta karamar hukumar kumbotso a kano.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da yake bayyanawa manema labarai a yammacin Laraba yace, sun sami nasarar cafke wanda ake zargi da kisan Rukayya mustapha.

Alfijr

Binciken da Sashen manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda da DSS suka gudanar ya kai ga cafke babban wanda ake zargi Abdulsamad Suleiman mai shekaru 18 a unguwar Dorayi Chiranchi Quarters a karamar hukumar Gwale Jihar Kano da abokin aikinsa

A bisa bincike mai zurfi, mahaifin wanda ake zargin ya amsa cewa a ranar 12/02/2022 da misalin karfe 4 na yamma, ya je gidan marigayiya ya same ta a kan gado.

Alfijr

Bayan ya gaisa sai yaga wayoyi guda uku (3) ya faki idonta ya dauke su, Daga bisani ta an kara da hakan, sai ta yi masa magana, sai ya yi amfani da wata katuwar tabarya, ya yi ta dukanta a kanta, sannan ya bugi ‘ya’yanta guda biyu ya tafi da wayoyin hannu.

Ya kuma kara da cewa ya baiwa abokin nasa daya daga cikin wayoyin hannu sannan ya sayar da sauran biyun akan Naira Dubu Goma Sha Biyu (N12,000:00).

Alfijr

An kama abokin nasa kuma ya amsa laifin sayar da wayar da aka ba shi ta marigayiyar akan Naira Dubu Biyu (N2,000:00).

DSP Kiyawa yace Za a gurfanar da shi gaban kotu bayan an kammala bincike.

Slide Up
x