Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceci Rayuka 91, Dukiya Ta N24. 9m A Watan Agusta

Alfijr ta rawaito ta rawaito Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci rayuka da dukiyoyi 91 da kudinsu ya kai Naira miliyan 24.9 daga gobara 29 da aka yi a watan Agusta.

Alfijr Labarai

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Abdullahi ya fitar ranar Juma’a a Kano.

Ya ƙara da cewar mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da gobara ta lalata dukiya ta Naira miliyan 8.3 a tsawon lokacin da ake bitar.

Ya ce ma’aikatar ta amsa kiraye-kirayen ceto 55 da kuma kiran karya 14 daga mazauna jihar.

Alfijr Labarai

Kakakin ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da ayyukan da suka shafi gobara domin hana afkuwar hadura.

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su rika tukin mota tare da kula sosai domin gujewa hadurra musamman a lokacin damina.

Slide Up
x