Hukumar NDLEA Ta Kona Hodar Iblis Da Ta Kama Ta Kimanin Naira Biliyan 194

Alfijr ta rawaito Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kone hodar iblis da sauran miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai naira biliyan 193 a Lagos.

Alfijr Labarai

Hukumar NDLEA ta ce ta kama hodar iblis mai yawan kilogiram 1,855 tare da cafke wasu masu safarar kwaya lokacin da ta kai wani farmaki a wani gidan ajiyar kaya a yankin Ikorodu na jihar Lagos.

Ga kamen da hukumar ta ce shi ne guda daya mafi girma a tarihin yaki da miyagun kwayoyi na Najeriya, ta wargaza shirin safarar kwayoyin da suka kai kimanin naira biliyan 194.

Hukumar ta kuma ce ta kama dillalan kwaya hudu ciki har da wani dan kasar Jamaika da manajan gidan ajiyar kayan.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *