Hukumar Shige Da Fice Ta Najeriya Ta Kori Ma’aikata 8, Ta Kuma Dakatar Da Mutane 18

Alfijr ta rawaito hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta ce ta kori ma’aikatanta takwas daga aikin, yayin da wasu goma sha takwas kuma aka kama su da laifuffuka daban-daban da suka shafi rashin da’a, cin hanci da rashawa da sauran ayyukan cin hanci da rashawa.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kenneth Kure, babban Sufeto na hukumar shige da fice a sashin hulda da jama’a, a madadin Kwanturolan Janar Isah Idris.

Sanarwar ta nuna cewa an dauki matakin ne biyo bayan amincewar da hukumar tsaro ta Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Board (CDFIB) ta bayar, inda ta nuna cewa halin da ma’aikatan ke yi ya kasance mara kyau kuma ba a yarda da shi a matsayin mambobin hukumar.

Wadanda abin ya shafa a matakin sun hada da babban Sufeto na shige da fice wanda aka umarce shi da ya tafi ritayar dole, yayin da wasu ma’aikata tara aka rage musu matsayi.

Bayan gamayya da kwamitocin, ma’aikata takwas da suka hada da Babban Sufeto na Shige da Fice (CSI), mataimakan Sufiritanda na Shige da Fice (DSI) biyu, mataimakan Sufiritanda na Shige da Fice II (ASI2) da kuma manyan mukamai uku an sallame su daga Sabis.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ma’aikatanta 100 da ke aiki a MMIA da ke Lagos an fitar da su daga filin jirgin nan take.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *