Wata Sabuwa! Jami’ar Jos Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki

Alfijr ta rawaito Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ke jami’ar Jos (UNIJOS) ta fara wani sabon yajin aiki don nuna rashin amincewa da biyan rabin albashin watan Oktoba da gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi wa mambobinta.

Hakazalika kungiyar ta kuma nuna rashin amincewarta da kin biyan bashin albashin watanni takwas da gwamnati ta ki yi na tsawon watanni 8 a yayin da kungiyar ta ke yajin aiki.

Sai dai kai tsaye kungiyar bata bayyana matakin a matsayin yajin aiki ba, ta ce dukkanin mambobinta su kaurace wa zuwa wurin aiki har sai an gyara zalincin da ake yi masu.

A wani bincike da jaridar Alfijr Labarai ta gabatar, ta gano majalisar zartaswar kungiyar ASUU ta kasa za ta yi wani zama a ranar Litinin mai zuwa domin tattaunawa kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux
[04/11, 5:30 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *