Ibtila’i: Mutane Da Dama Sun Mutu Wasu Sun Jikkata Yayin Da Motar BRT Ta Yi Karo Da Jirgin Ƙasa A Lagos

Alfijr ta rawaito Mutane biyu sun mutu wasu da dama kuma sun jikkata bayan da wani jirgin fasinja ya murkushe wata motar ma’aikatan gwamnatin jihar Legas a unguwar PWD da ke jihar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na safiyar yau Laraba, 9 ga Maris, 2023.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san yadda motar BRT ta samu hanyar zuwa titin jirgin ba.

Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (LASTMA) a jihar Legas, Taofiq Adebayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma bayyana cewar ana ci gaba da aikin ceto.

“Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da motar bas ta cika makil da ma’aikatan gwamnati da ke zuwa ofishin da safiyar yau,” in ji Adebayo.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *