Ibtila’i Yadda wata motar Kano Line ta kama da wuta akan hanyar zuwa Kaduna

FB IMG 1735828685523

Daga Aminu Bala Madobi

Motar mallakin Kano Line ce, wadda ta taso daga Kano Zuwa Kaduna tayi hadarin ne a Makarfi kuma kawo izuwa yanzu anata kokari don shawo kan wutar

Rahotonni sun ce suwa wannan lokacin hada wannan rahoto ana kokarin kashe wutar dake ta faman ci ganga-ganga, sai dai wani shedar gani da ido ya tabbatar da cewa anyi kokarin fitar da mutane 9 daga cikin motar kafin wuta ta tashi gadan gadan, amma akwai wasu da dama da wutar ta kama su.

Sai dai tuni jami’an bada agajin gaggawa suka yi azama domin kawo wa motar da mutanen ciki dauki, sa idai zuwa yanzu akwai fasinjoji da dama da suka makale cikin motar.

Allah ya tsare hakan a gaba

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *