Yadda al’umma Suka yi Dafifi Wajen Taron Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Bayan Dawowa Daga Ziyarar Aiki Da Yaje Kasar Egypt

IMG 20250102 WA0640

Dubbunan al’umar jihar Kano ne suka tari Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan dawowarsa daga kasar Egypt a wata ziyarar aiki da ya kai.

Masoya sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sunyi cikar dango tareda cika tituna domin yin lale marhabun da dawowar Sarkin gida lafiya.

A kalla dai an shafe awanni masu yawa daga filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano (MAKIA) zuwa gidan Mai Martaba Sarkin dake Nassarawa sakamakon yawan al’umar da suka tareshi babu masaka tsinke.

Idan dai za’a Iya tunawa Kimanin makonni biyu Kenan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yabar Kano zuwa kasar ta Egypt domin ziyarar aiki.

A lokacin ziyarar ne ma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin kungiyoyi daban daban na Yan Najeriya dake zaune a kasar ta Egypt.

Kazalika Sarkin ya gana da jami’ai na Gwamnatin Kasar da mambobin diflomasiya da daidaikun mutane wadanda suka tattauna akan harkokin kasuwanci da tattalin arziki da Kuma cigaban jihar Kano da Najeriya.

Bayan saukar sa a fadarsa dake Nassarawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa dumbin al’umar da suka tareshi tareda yimusu addu’ar fatan alheri.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi amfani da wannan dama wajan Kara Jan hankali matasa su cigaba da kasancewa masu da’a da ladabi da biyayya da son junansu da Kuma Zaman lafiya.

Ya sake yabawa al’uma bisa yadda suka fito cikin ladabi da nutsuwa domin nuna godiyarsu ga Allah da nuna farin cikinsu bayan dawowarsa daga ziyarar aiki a kasar Egypt.

E Signed.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to His Highness the Emir of Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
2/01/2025

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *