Inda Ranka! Wata Bazawara Ta Maka Mahaifinta A Gaban Mai Shari’a

Alfijr

Alfijr ta rawaito, wata bazawara mai suna Sadiya yar shekara 25 a ranar Laraba data gabata 23/02/2022 ta maka mahaifinta Malam Usman a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke zama a Rigasa, jihar Kaduna, kan zarginsa da take da yi mata auren dole.

Alfijr

Sadiya ta sanar da kotun cewa wannan shi ne aurenta karo na uku, mahaifina ne ya shirya tare da daura min auren dole ba tare da barin na san wanda zan aura ba tun farko.

Ta shaidawa mai shari’a cewar, aurena na farko, na biyu da na uku duk auren dole ne da mahaifina ya shirya min ba a son raina ba.

Alfijr

Don haka, ba zan cigaba da zama ba, ina son wannan kotun da ta tsinke igiyoyin auren, a cewar Sadiya.

Vanguard ta ruwaito, mahaifin sadiya mal Usman ya ce yar tasa da kanta ta kawo masa mutumin gida amma daga baya tace bata son shi.

Alfijr

Ya kara da cewa, ikirarin da take yi na cewa bata san shi ba duk karya ne, sannan yanzu haka ban san inda diyata take da zama ba, ta bar gida a ranar aurenta, don haka nake rokon kotu da ta umarce ta da ta dawo gida da gaggawa,” inji mahaifinta.

Sadiya ta sanar da kotun cewa a halin yanzu ta na zaune ne a yankin Unguwan Sarki da ke jihar.

Alfijr

Alkalin kotun, mai shari’a Malam Salisu Abubakar Tureta bai amsa bukatar Mal Usman ba, amma ya umarci Sadiya da ta koma gidan hakimin Rigasa.

Mai shari’a ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar goma ga watan Maris domin mai korafin ta gabatar da shaidunta.

Slide Up
x