An Yanka Ta Tashi! Kotun Abuja Ta Sake Bada Umarnin Garkame Jaruma Mai Kayan Mata A Gidan Yari

Alfijr

Alfijr ta rawaito, kotun Upper Area, Zuba da ke Abuja ta soke belin da aka bayar na fitacciyar mai sayar da maganin mata Hauwa Saidu wadda aka fi sani da Jaruma a ranar 28 ga watan Janairu bayan shafe kwanaki hudu a gidan yari.

Alfijr

Alkalin kotun, Barista Ismail Abdullahi Jibrin, ya janye belin da aka bayar tare da bayar da umarnin a sake tsare ta bayan da ita da lauyanta suka kasa gurfana a gaban kotu a yau, sannan kuma suka kasa tura ko wane wakili.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Jaruma a gidan yari na Suleja, har zuwa ranar 17 ga Maris, 2022 wadda ita ce sabuwar ranar da za a ci gaba da sauraron karar.

Alfijr

Tun da farko dai alkalin kotun ya dakatar da shari’ar saboda babu daya daga cikin lauyoyin Jaruma da ya halarci kotun.

Wani Lauyan da ke harabar kotun ya roki alkalin da ya yi hakuri domin Jaruma da lauyoyinta za su zo nan gaba.

Alfijr

Bayan shafe sa’o’i biyu ana jiran alkali a fusace ya janye belin ta tare da bayar da umarnin a sake kama ta.

Slide Up
x