INEC Ta Bayyana Wuraren da za a sake zaɓen sanatoci a Najeriya

Alfijr ta rawaito Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta fitar da jadawalin zaɓaɓɓun sanatocin da suka yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Cikin jadawalin da Inec ta fitar, an tabbatar da zaɓukan da aka yi na mazaɓu 109, guda bakwai kuma za a sake yin su, yayin da kujera ɗaya kuma take ba kowa a kai saboda mutuwar ɗaya daga cikin masu takara.

A jerin sunayen, Jam’iyyar APC ta lashe mafi yawan kujeru da 55 sai PDP da take da kujeru 33, Jam’iyyar LP kuma ta samu kujeru 7.

Shugaban Inec, Mahmood Yakubu a jawabin da ya yi na baya-bayan nan a ganawarsa da kwamishinonin hukumar zaɓe a Abuja, babban birnin Najeriya, ya ce jam’iyyu takwas ne suka samar da sanatoci a zaɓen da ya gabata.


Jam’iyyun sune APC, PDP, APGA, SDP, Labour, NNPP, ADC da YPP.

A cewar Inec, za a sake gudanar da zaɓe a mazaɓun da ba a sanar da wanda ya yi nasara ba bayan zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokoki a jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan hukumar zaɓe mai kula da ɓangaren yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Festus Okoye ya sanyawa hannu, “hukumar tana sane da cewa ba a bayyana sakamakon zaɓen wasu mazaɓu ba na sanatoci. Hukumar tana tattara bayanan mazaɓun da abin ya shafa.

Ga dai jerin mazaɓun da za a sake gudanar da zaɓen:

Mazaɓar Kebbi ta Arewa

Mazaɓar Plateau ta Tsakiya

Mazaɓar Sokoto ta Arewa

Mazaɓar Sokoto ta Kudu

Mazaɓar Sokoto ta Gabas

Mazaɓar Yobe ta Kudu

Mazaɓar Zamfara ta Tsakiya

Mazaɓar Enugu ta Gabas inda ɗaya daga cikin ƴan takarar ya mutu.

BBC


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *