Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayar da umarni ga dukkan Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (RECs) da su dakatar da duk wani shiri da ya shafi atisayen sabunta rajistar masu zaɓe da aka tsara gudanarwa a faɗin Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan da a baya hukumar ta sanar da cewa za ta fara aikin sabunta rajistar masu zaɓe a ranar 13 ga Afrilu, 2026.
An bayyana cewa shirin na daga cikin muhimman matakan da INEC ke ɗauka domin sabunta kundin rajistar masu zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata wasiƙa da sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, INEC ta buƙaci RECs da su fara shirye-shiryen gudanar da aikin.
Daga cikin shirye-shiryen da aka ambata akwai samar da ma’aikatan wucin gadi da na dindindin, tare da tanadin na’urorin rajistar masu zaɓe na zamani (IVED) domin tabbatar da ingantaccen aiki.
Haka kuma, hukumar ta fitar da cikakken jadawalin yadda za a gudanar da aikin.
Bisa ga jadawalin, za a fara ne daga matakin ƙananan hukumomi daga ranar 13 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu.
Bayan haka, za a ci gaba da aikin a matakin cibiyoyin rijistar daga ranar 5 zuwa 11 ga Mayu.
A ƙarshe, za a kammala aikin a rumfunan zaɓe daga ranar 13 zuwa 19 ga Mayu.
Sai dai duk da wannan shiri, a sabon umarnin da hukumar ta fitar, ta ce dole ne a dakatar da duk wani aiki da ya shafi shirye-shiryen sabunta rajistar masu zaɓe har sai an sake bayar da wata sanarwa daga babban ofishinta.
Bugu da ƙari, INEC ta sanar da sauyin tsarin taron da ta shirya yi da RECs.
Taron wanda tun farko aka tsara gudanarwa a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026, da ƙarfe 11 na safe a zahiri, yanzu za a gudanar da shi ne ta yanar gizo ta hanyar amfani da manhajar Zoom.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan dakatarwa na iya zama wani mataki na sake duba shirye-shiryen ko kuma gyara wasu muhimman batutuwa da suka shafi aikin. Duk da haka, INEC ba ta bayyana takamaiman dalilin dakatarwar ba a hukumance.
Ana sa ran cewa hukumar za ta sake fitar da sabuwar sanarwa nan gaba, wacce za ta fayyace sabon jadawali da kuma matakan da za a ɗauka domin ci gaba da aikin sabunta rajistar masu zaɓe cikin tsari mai inganci da gaskiya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t