Jam’iyyar APC Ta Bukaci ‘Yan Sanda Da Su Kama Wasu Fitattun Mutane 16 Cikin Gaggawa A Kano

FB IMG 1707908149590

A wata sanarwa da ta fito daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, ya nuna yadda jam’iyyar ta aika saƙo ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, domin kama wasu fitattun mutane 16 a jihar bisa zarginsu da tunzura jama’a a kan jam’iyyarsu ta shafukan sada zumunta.

Alfijir labarai ta rawaito wasikar mai kwanan wata 5 ga watan Janairu, 2024, mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar APC na jihar, Ibrahim Zakari, ta bukaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta kama mutane goma sha shida tare da gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda jam’iyyar ta rubuta.

A cewar wasikar, jam’iyyar na da kwarin guiwar cewa dan takararta na gwamna, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna zai bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris din 2023, kuma a kan haka ne jam’iyyar ta baiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya izini la’akari da wasika a matsayin umarni.

Wasikar kamar haka: “A madadin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, muna rokon da a binciko mutanen da aka jera sunayensu a kasa tare da kama su nan take bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar Juma’a 12 ga Janairu, 2024, wadda za ta bayyana Dr. Nasiru Yusuf. Gawuna a matsayin mai nasara.

“Muna kuma rokon hukumar da ta gaggauta gabatar da kararraki tare da zarginsu da amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen furta kalamai marasa dadi, da ke iya tada rikici da tunzura mutane kan gwamnatin APC.

Muna da gamsassun hujjoji akan rubuce-rubucen su. Za a aiko muku da sunan kotun da ya kamata ku gabatar da kararsu a lokacin da ya dace.

 1. Salisu Yahaya Hotoro
 2. Aliyu Dahiru Aliyu
 3. Kabiru Sa’idu Dakata
 4. Hon. Sunusi bature dawakin tofa
 5. Nasiru Zango
 6. Sufyan Safjamil Kabo
 7. Hajiya A’in Jafaru Darmanawa
 8. Alhajiji Nagoda

Hon Ibrahim Zakari

 1. Ibrahim Zakari Zawaciki
 2. Sani Musa Danja
 3. Hon. Auwalu Lawan Aranposu
 4. Sunusi Osca
 5. Kwankwason Dakata
 6. Ishak Abdul
 7. Aminu Abdullahi Kima
 8. Habu Tabule

“Za a aiko muku da adiresoshin gida da ofis na mutanen da aka lissafa, na gode.”

Kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun kori Gwamna Yusuf tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben a baya.

Sai dai kotun koli ta yi watsi da hukuncin kotun zabe da kotun daukaka kara tare da tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

FB IMG 1707908142706
📸 APC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *