Jarumi Nuhu Abdullahi Yayi Raddi Ga Naziru Sarkin Waka Kan Masu Cinye Kudi A Kannywood

Alfijr

Alfijr ta rawaito Jarumi Nuhu Abdullahi ya mai martani ga Naziru Sarkin Waka Kan batun da ya yi kan masu shirya fina finai A Kano

Alfijr

Hirar da BBC tayi da ɗaya daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood Ladi Cima, hirar ta jawo cecekuce a tsakanin al’umma da kuma manyan Jaruman Kannywood har ta saka an fara mayar da martani ta kakkausar murya.

Mawaki Naziru Sarkin Waka ya yi fashin baki sosai a kan haka kuma da alama ya goyi bayan hirar Ladin Cima kan rashin biyan hakkin aiki yadda ya kamata ga Jarumai.

Alfijr

A nasa batun Jarumi Nuhu Abdullahi, yayi nashi maganganun inda yake sukar Naziru da cewar ya fara yiwa Yayan sa Aminu Saira waazi game da biyan hakkin kudin maaikata kafin yazo ya ce wani abu.

Wata Sabuwa kenan! To me kalaman Nuhun suke nufi kenan?

Slide Up
x