Alfijr
Alfijr ta rawaito, Kakakin ’Yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanar da manema labarai game da cafke matasan su 3 da suka fitini unguwar Kurna Tudun Fulani da suke a garin kano a ranar 8 ga watan Fabrairu 2022.
Alfijr
Dubun bata garin ta cika ne a lokuta daban-daban; a unguwar Dan Rimi da unguwar Zage tsakanin ranar 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu.
Kiyawa, ya ce tuni wadanda ake zargin suka amsa tuhumar da ake musu na aikata manyan laifuka, inda suka raunata mutane da dama ya kuma kara da cewar, rundunar na gudanar da bincike kan irin miyagun ayyukan da matasan suka tafka don gurfanar da su gaban shari’a.
Alfijr
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun addabi unguwanni da dama a cikin Kano, musamman unguwar Kurna Tudun Fulani da ke Karamar Hukumar Ungogo, inda suka raunata mutane da dama Hadi da kwacen wayoyin al umma.