Jihar Kano Zata Karbi Bakuncin Babban Taron Majalisar Ayyuka Na Kasa karo Na 28

Alfijr ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf gudanar da taron majalisar ayyuka na kasa karo na 28.

Alfijr Labarai

Gagarumin taron z a a fara gabatar dashi ne daga litinin 22nd August 2022, sannan kuma za’a kare ranar Juma’a 27th August 2022

Kwamishinan ayyuka da raya ababen more rayuwa na jihar Engr. Idris Wada Saleh ya bayyana hakan a ofishin sa a yau.

Engr. Wada Saleh ya ce taron na shekara-shekara ne da ke hada dukkan masu ruwa da tsaki a fadin tarayyar kasar nan jihohi 36, ciki har da Abuja tare da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi bangaren ayyuka.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne zai zama babban bako na musamman, yayin da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, SAN zai jagoranci taron.

Alfijr Labarai

Karamin Ministan ayyuka da gidaje, Hon. Umar Ibrahim El-Yakub da kwamishinoni da manyan sakatarorin na ma’aikatun ayyuka a fadin kasar nan, shugabannin hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki ana sa ran za su halarci taron na kwanaki 5 da za a yi a otal din Bristol Palace.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, taken taron na bana shi ne.

Kakar Kammala Manyan Aiyuka

Sa hannun: Muhammad Galadima Jami’in Watsa Labarai na Ma’aikatar Ayyuka da Raya ababen more rayuwa ta Jihar Kano 21/8/2022

Slide Up
x