“Ka yi murabus, ka daina tayar mana da zaune-tsaye a Jam’iyyarmu — Jam’iyyar APC ta gargadi Wike

IMG 20260105 WA0641

Daga Aminu Bala Madobi

Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, ya yi kakkausar suka ga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, inda ya bukace shi da ya daina abin da ya kira yunkurin dagula harkokin jam’iyyar APC.

Bashiru ya ce idan har Wike ba zai iya dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gida na APC ba, to ya fi dacewa ya yi murabus daga muƙaminsa na minista domin kauce wa rikitar da tafiyar jam’iyyar da gwamnatin da take jagoranta.

A cewarsa, jam’iyya mai mulki na buƙatar haɗin kai da biyayya ga ƙa’idoji, ba wai ayyukan da za su haddasa rarrabuwar kai ko rikici ba. Ya jaddada cewa duk wani ɗan APC, ko mai riƙe da muƙami a gwamnati, dole ne ya mutunta tsarin jam’iyya da shugabancinta.

Jaridar Alfijir Ta Rawaito Cewar Maganganun sun zo ne a daidai lokacin da ake zargin Wike da yin tasiri da tsoma baki a wasu al’amuran jam’iyyar APC, abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *