Kadan Daga Cikin Bayanai 47 Da Shugaba Buhari Ya Gabatar A Ranar Samun ƴancin Najeriya

.

Alfijr ta rawaito Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa na karshe a ranar da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ƴancin kai.

Alfijr Labarai

A irin wannan rana ƙasar ta samun ƴancin kai a matsayin Najeriya wacce turaawan mulkin mallaka suka bayar tun daga 1960

1. Haɓaka tattalin arizikin Najeriya inda shugaba Buhari ya ce tun a lokacin da aka zaɓe shi, ya yi alƙawarin haɓaka tattalin arziƙi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma inganta tsaro.

Kan waɗannan alƙawuran, gwamnatinsa ta kuma sha alwashi yin tsayuwar daka wajen ganin cewa ta cire Ƴan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekara goma.

Sai dai ya bayyana cewa da taimakon Ubangiji, gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari wurin cika waɗannan alƙawuran da goyon bayan ƴan ƙasar da dama amma duk da haka a cewarsa kwaliyya ba ta kammala biyan kuɗin sabulu ba.

Alfijr Labarai

Buhari ya bayyana cewa ɗaya daga cikin wuraren da gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari shi ne bangaren yaƙi da cin hanci inda ya ce sakamakon inganta ɓangarorin yaƙi da cin hanci da kuma taimakon ƙasashen waje an mayar da kuɗaden haram masu yawa da aka sace aka fitar waje.

Ɓangaren tsaro kuma, ya bayyana cewa an yi ƙoƙari wajen rage rikicin da ake yi a arewa maso gabashin ƙasar, da rikicin ƴan tayar da ƙayar baya a yankin Neja Delta da kuma rikice-rikicen ƙabilanci a wasu sassa na Najeriya da sauran matsalolin da ke yi wa ƙasar barazana, da kuma fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga har sau biyu.

Alfijr Labarai

2. Buhari ya tabbatar da cewa sun bai wa ɓangaren noma fifiko ta hanyar fito da ƙanana da matsakaitan tallafi da suka samar da ayyuka ga miliyoyin mutane.

Kamar su Anchor Borrower wanda ƴan kasa sun samu tallafi daga ko ina cikin Kasar, sai samun wadataccen abinci da kuma ɗaukar noma a matsayin sana’a.

Ya kara da cewa fitar da kayayyaki da ƙasar ke yi musamman amfanin gona da sauran abubuwa na kimiyya da fasaha za su taimaka wa kasuwar hada-hadar kuɗi ta ƙasar.

Alfijr Labarai

3. Buhari ya bayyana cewa yana matuƙar baƙin ciki sakamakon cikas da ake samu la ɓangaren ilimin jami’ oin ƙasar.

“Ya kara da cewa, Ina kira ga ƙungiyar ASUU da ta koma aji kuma ina ba su tabbacin cewa zan share musu hawayensu da ɗan abin da muke da shi duk da muna rashin kuɗi,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wurin magance matsalar wadda aka shafe shekara 11 ana fama da ita.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙari wurin tattara kuɗi a ciki da wajen ƙasar domin tallafa wa ɓangaren ilimi don tabbatar da cewa ƴan ƙasar sun samu ingantaccen ilimi.

Alfijr Labarai

4. Shugaba Buhari ya yi alƙawarin ƙara inganta harkar zaɓe a ƙasar a yayin da ake fuskantar zaɓen 2023 a gaba.

Shugaban ya bayyana cewa duk wani ci gaba da aka samu a ƙasar idan ba a zaɓi shugabanni ta ingantacciyar hanya ba duk wani ƙoƙari da aka yi ba zai isa ba.

Ta kara kira ga ƴan takara da su gudanar da yaƙin neman zabensu cikin lumana da kuma kiyayewa daga kalaman ɓatanci ga juna.

Alfijr Labarai

5. Shugaba Buhari ya bayyana ƙoƙarin gwamnatinsa, wurin inganta ɓangaren kiwon lafiya, musamman idan aka yi duba da lokacin annobar korona, ƙasar ta taka rawar gani da har ya sa ƙasashen duniya suka jinjina mata.

Shugaban ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya da ta ba mara ɗa kunya ta hanyar juriya da mayar da hankali bayan duniya ta yi hashen cewa tana daga cikin ƙasashen da annobar korona za ta yi wa ɓarna

6. Ya kara da cewa Tuni dai gyare-gyare a ma’aikatun gwamnati ke samar da sakamako musamman wajen gudanar da ayyuka.

A kan wannan bayanin, ina kira ga jama’a da su nemi ayyukan da ya shafi ‘yan kasa daga hukumomin da abin ya shafa.

Alfijr Labarai

7. A bangaren kasa da kasa, mun ci gaba da cin gajiyar dandalinmu na bangarorin biyu da na bangarori daban-daban, don lalubo hadin gwiwa da kasashen abokantaka da abokan hulda a duk lokacin da wadannan fannonin hadin gwiwar suka kasance da amfani ga Nijeriya.

8. ‘Yan uwa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata mun shaida kuma mun shawo kan kalubale masu yawa da za su lalata al’ummarmu.

Duk da haka, rashin gajiyawa na al’ummar Najeriya ya tabbatar da cewa mun shawo kan kalubalen da muke fuskanta. In Ji Buhari

9. ​​Ya ƙara da cewar, a cikin ruhi na nake kira ga dukkanmu da mu fito da mu a daidaiku da kuma a dunkule wajen tunkarar dukkan al’amuran ci gaban mu.

19. Shugaba Muhammadu Buhari ya ce An Zaɓe ni ne don yin hidima, tare da sauran yan siyasa, domin samar da ingantacciyar Najeriya wadda muka yi tare da goyon bayan ‘yan Najeriya.

Alfijr Labarai

A karshe ya ce Allah madaukakin Sarki da al’ummar Nijeriya nagari sun ba mu goyon baya wajen aza harsashin gina Nijeriyar da muke fata.

Ina godiya gareku baki daya Allah ya albarkaci tarayyar Nigeria.
Muhammadu Buhari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *