Kakakin Rundunar Yan Sandan Nigeria Ya Yi Gargadi Da Jan Kunne Ga‘ƴan sandan Bisa Umarnin IGP

Alfijr ta rawaito Kakakin rundunar ƴan Sandan Nigeria ya gargadi ‘yan sandan da ke tsayawa bincike a kan tituna kan kada su saba wa umurnin babban sufeton ‘yan sandan ƙasar

Alfijr Labarai

CSP Olumuyiwa Adejobi, wanda ke zaman mai magana da yawun hukumar ƴan sanda ta kasa, ya gargadi jami’an rundunar da su guji aikata rashin da’a, kamar shiga tasha da bincike cikin kayan gida wato (Mufti).

Kakakin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata da ta gabata, inda ya ce rashin da’a ne kuma babban cin zarafi ne ga umarnin babban Supeton ƙasar, tsayawa yayin binciken abababen hawa a gefen hanya a cikin mufti.

Ya kuma yi nuni da cewa, ana sa ran kowane jami’in ‘yan sanda da ke da alhakin sanya kaya yadda ya kamata a lokacin da ya fito bakin titi domin duba motocin da ke tafiya.

Alfijr Labarai

“Mun fada a lokuta da yawa cewa kada wani dan sanda ya tsaya kan hanya ya tsaya ya yi bincike a cikin mufti.

Rashin ƙwarewa ne kuma babban keta umarnin Supeton ne, kamar yadda umarni ya gabata.

“Kowane dan sandan da ke gudanar da ayyukansa kamar tsayawa da bincike, sintiri, dole ne ya kasance sanye da kayan aiki domin gane waye shi a sauƙaƙe, saboda dalilai da yawa.

Don haka muna Allah wadai da wannan aiki.

Alfijr Labarai

Ya kara da cewa, za mu ci gaba da yin abin da ake bukata bisa horo, da da’a tare da kyawawan halaye a cikin ayyukan mu. Mun gode. In Ji shi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *