AZMAN Air Ya Bayyana Nasarorin Da Ya Samu A Aikin Hajjin Bana 2022, Duk Da Matsalolin Da Suka Samu A Kano

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito kamfanin Jirgin sama na AZMAN Airline ya bayyana aikin hajjin na shekarar 2022 cikin nasara bayan jigilar maniyyata 7,300 da kuma rundunar sojojin da hukumar HAHCON ta ware wa kamfanin daga jihohi 16 na tarayyar Najeriya.

Alfijr Labarai

Ko odinetan aikin Hajji na kamfanin jiragen sama na Azman, Engr Nuraddeen Aliyu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi a Kano.

A cewarsa, duk da cewa sun bayyana a makare, amma sun sami damar jigilar dukkan fasinjojin nasu, sai dai wasu daga Kano saboda kin amincewar da jihar ta yi a matsayin jigilarsu.

Jihohin su ne; Kaduna, Kano, Yobe, Ekiti, Ondo, ciki har da jihohin Kudu  maso Gabashin kasar nan.

Duk da an fara a makare, mun sami damar haduwa ba tare da mun zauna da kowa a makale ba.

Alfijr Labarai

Hakazalika mun dauki Alhazan jirgin yawo kimanin 2500 kuma munyi Hulda dasu cikin aminci Anji dadin huldar, mun kaisu mun dawo dasu akan lokacin da muka dauka duk kansu mun dauke su daga kano ne, alhazan sun fito daga jihohin sokoto, kebbi, Gombe, Bauchi, maiduguri, Kaduna, yobe, kano da sauransu! Inji shi

Matsalar Kano kuma ta faro ne a lokacin da suka ki karbarmu a matsayin nasu, wanda ya sa muka fara da wasu jihohi.

A karshen aikin ne suka karbe mu kuma muka kwashe su na farko alhazai 400 amma kashi na biyu ya samu jinkiri saboda rashin shiri.

Bisa la’akari da halin da ake ciki a wancan lokacin da kuma wa’adin da Hukumomin Saudiyya suka bayar, sai muka rubuta wata takarda zuwa ga NAHCON ta sake samar da wani lokacin da kamfanin jirgin da zai ceto Alhazan Kano.

Sun amince da bukatarmu, amma hakan bai yi nasara ba, don haka matsalar ba daga wurinmu ba ce,” inji shi.

Sai dai duk da wasu matsaloli da aka samu a lokacin da aka fara aikin, fuska ta biyu ta samu gagarumar nasara bayan dukkan fasinjoji tare da karin jami’an NAHCON kimanin 150 sun yi nasarar komawa gida a kan jirgin.

Alfijr Labarai

Aliyu, ya kara da cewa, babban kalubalen da aka fuskanta a lokacin aikin Hajjin 2022 shi ne ci gaba da fuskantar karancin man jiragen sama a Najeriya wanda ya tilasta musu komawa Lagos don neman mai, kafin su koma Jiddah, lamarin da ya haifar da tsaikon da bai kamata ba.

Nuraddeen ya ci gaba da alakanta jinkirin shirye-shiryen da Hukumar Alhazai ta Najeriya ta yi da kuma jinkirin da gwamnatin Saudiyya ta bayar a matsayin manyan dalilan da ke kawo tsaikon.

Ya, kuma tabbatar da cewar kamfanin nasu yayi alkawarin samar da ingantacciyar hidima a ayyukansu na gaba da izinin Allah

Slide Up
x