Kashe Rukayya Mustapha A Kano! Gwamna Ganduje ya Umarci Bankado Wadanda Suka Yi Kisan

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya umurci hukumomin tsaro da su bankado wadanda suka kashe Rukayya Mustapha, matar aure da wasu da ba a san ko su waye ba suka kashe.

Alfijr

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin da yake jajantawa iyalan mamacin a unguwar Dorayi Quarters dake karamar hukumar Kumbotso a jihar.

Mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya wakilci Gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.

Alfijr

Abin takaici ne muka samu labarin rasuwar marigayiya Rukayya Mustapha… Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu bar wani abu ya tafi a haka ba, kullum kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar shine a gabanmu

A madadin gwamnati da al’ummar jihar ina Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar Allah ya jikanta da Jannatul Firdaus tare da baiwa iyalanta kwarin guiwar jure rashinta

Alfijr

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayyana cewa kawo yanzu an kama mutane 5 da ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka yi kisan.

Kwamishinan ya kara da cewa, wadanda suka yi ta’ammali da miyagun kwayoyi ne suke aikata irin wadannan laifuffuka, shi ya sa suke kame wadanda suke safarar miyagun kwayoyi domin dakile sake afkuwar lamarin.

Alfijr

Dikko ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su rubanya kokarinsu na ganin an tabbatar da hana faruwar irin wadannan laifuka.

Tawagar ta kunshi kwamishinoni da Daraktan DSS Alhassan Muhammed da shugaban karamar hukumar Kumbotso Hassan Garban Kauye.

Slide Up
x