Abdulmalik Ya Musanta Kashe Hanifa A Kotu

Alfijr

Alfijr ta rawaito Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da kisan Hanifa mai shekara 5 a Kano, ya musanta zargin kasheta.

Alfijr

Abdulmalik wanda ake zargi da sace da kashe Hanifa, ya musanta zargin da aka karanto masa shi da wasu mutum biyu a kotu yayin da ake ci gaba da shari’ar a yau Litinin.

Abdulmalik Tanko da Hashimu sun musanta zargin garkuwa da Hanifa da bata guba da kuma binne gawarta a wata makaranta kamar yadda aka ganu su a bidiyo suna bayani.

Alfijr

Zargin hada baki ne kawai suka amsa yayin da aka karanto musu shi

Matar Abdulmalik, Fatima, wadda ke cikin waɗanda ake zargin, ta musanta zargin da aka karanto mata na rubuta wasiƙa ga iyayen Hanifa cewa ana buƙatar kuɗin fansa naira miliyan 6 a madadin Abdulmalik Tanko.

Haka nan, Fatima ta musanta duka zarge-zargen da aka karanto mata.

Alfijr

A zaman da aka yi ranar 7 ga watan Fabarairu waɗanda ake zargin suka nemi gwamnati ta ba su lauyan da zai kare su. Barista M. L. Usman daga ƙungiyar Legal Aid da Barista P. A. Ademakun ke kare mutanen.

Lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan sun nemi kotu ta ba su damar kawo shaidunsu a zama na gaba.

Alfijr

Yayin da mai Shari’a Sulaiman Naabba ya ɗage zaman kotun zuwa 2 da 3 ga watan Maris mai zuwa don sauraron shaidu.

Slide Up
x