Alfijr
Kamar yadda ta saba a yau Asabar, 16 ga watan Afrilu 2022,
Alfijr ta rawaito kungiyar hadinkai da zumunci KHZ Foundation, ta rabawa marayu dari da Hamsin (150) kayan masarufin azumi a unguwanni biyar na jihar Kano, unguwannin sun hada da Tukuntawa bakin dogo, sabuwar gandu, gyadi gyadi farin masallaci, hotoro tishama da kuma Walalambe.
Rabon tallafin ya zo ne ranar Asabar 15 ga Ramadan, wanda ya samu halartar jigajigan kungiyar karkashin jagorancin Alh. Abdussalam Kayarima
A jawabinsa da ya gabatar a wajen rabon tallafin Alh. Abdussalam Kayarima ya godewa duk Manbobin kungiyar da suka samu damar halartar bikin sannan ya jawo hankalinsu akan a cigaba da bayar da hadin kai musammam wajen biyan kudin wata wata, saboda da irin su ne ake amfani da su, da kuma kudin da aka samu a gidauniyar da aka kafa wanda jimlar kudin yakai kusan Naira Dubu Dari Takwas.
Alfijr
Shugaban ya kara da cewa bayan sallah kungiyar Hadinkai da Zumunci (KHZ) za ta yi wani sabon shiri na ‘yanto ‘yan gidan yari ta hanyar biya musu tara.
Daya daga cikin Marayun da su ka samu tallafin Halima Sulaiman dake unguwar Walalanbe ta nuna matukar farin ciki da wannan tallafi da ta samu Taliya, Shinkafa da kuma Man girki, ta yi addu’a ga kungiya akan Allah ya daukaka ta.
Alfijir
Kakakin yaɗa Labaran kungiyar Baba Balarabe yayi addu’ar fatan alheri kowa, da kuma Allah ya mayar da kowa gidajensu lafiya