Alfijr
Alfijr ta rawaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da wa’adin sa’o’i 24 ga duk wani dan siyasa da ke neman tsayawa takara a Zabe mai zuwa na 2023.
Sanarwar da Abbas Anwar ya fitar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya Umarci duk Wani Dake Rike da Mukamin Siyasa a Gwamnatin sa kuma yake son Takara daya aje aikinsa daga yanzu zuwa Litinin 18 ga watan Afrilu da muke ciki.
Cikin wata Sanarwa mai dauke dasa hannun Daraktan Yada Labaran Gwamna, Malam Abba Anwar yace Hakan ha zama wajibi duba da tanade tanaden Sashi na 84 (12) cikin Baka na Sabuwar Dokar Zaɓen Kasar nan.
Alfijr
Kadan daga cikin wadanda suka fara sauka a yau.
Hon Musa Iliyasu
Hon Murtala Sule Garo
Hon Nuraq Muhammadu Dan kadai
Hon Faruk Sule Garo
Hon Mukhtar Ishaq Yakasai
Hon Sanusi Sa’idu Kiru
Hon Ibrahim Ahmad Karaye