Kotu Ta Daure Wasu Dattijai Masu Shekaru 65, Da 52, Bayan Samunsu Da Yiwa Yarinya Cikin Shege

Kotun Majistare da ke zamanta garin Zaria unguwar Chediya, ta tasa keyar wani tsoho mai shekara 65 da kuma wani mai shekara 52 zuwa gidan yari saboda zargin yi wa wata yarinya ciki.

Alfijr Labarai

Wanda ake zargin dan Shekaru 65 mai gadi ne a wani gidan, shi kuma dayan mai shekara 52, dan acaba ne, sai na ukunsu, dukkansu mazauna garin Tsibiri ne a Giwa ta Jihar Kaduna.

Sufeto Mannir Nasir, shi mai shigar da kara, ya shaida wa kotu cewa a ranar 13 ga watan Satumba 2022, wani mai suna Alhaji Nura Yusuf da ke garin Tsibiri ya kai koke zuwa ofishin ’yan sanda da ke Giwa cewar a ranar 1 ga watan Agusta 2022 bayan ya tsananta binciken ’yarsa don sanin wanda ya yi mata ciki sai ta bayyana masa sunayen mutum uku.

Kuma laifin da ake zargin su da aikatawa ya saba da sashi na 368 na doka final kod ta Jihar Kaduna ta shekarar 2017 wadda kuma bai kamata a bayar da su beli ba.

Alfijr Labarai

Da alkali ya tambaye su kan zargin da ake musu, duk kansu ba su musanta tuhumar da ake yi musu ba.

Da ta ke bayani mai Shari’a Docas Kitchner ta tsayar da ranar 17 ga watan Oktoba,  2022 domin yanke hukunci kamar yadda mai gabatar da kara ya bukata duba da wadana ake zargin ba su musanta tuhumar ba.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *