Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa ta umarci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da ta saki matashiyar nan Walida Abdulhadi tare da miƙa wa ’yan sanda jami’inta da ake zargi da sace ta domin gudanar da bincike.
A bayan nan dai an yi ta cece-kuce kan shari’ar ta shafi zargin wani jami’in DSS, Ifeanyi Onyewuenyi, da yin garkuwa da kuma lalata da Walida mai shekara 16 har ta haifa masa jaririya.
Batun matashiyar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan da wasu gungun lauyoyi suka shigar da ƙara suna zargin jami’in DSS ɗin da laifin “sacewa da yin lalata da kuma sauya mata addini.”
Idan dai ba a manta ba, tun a watan Janairun da ya gabata ne wata Kotun Majistare da ke zaune a Haɗejia da ke jihar Jigawa, ta ba wa DSS umarnin kama jami’in nata, wanda ake zargi da yi wa yarinyar fyaɗe ya kuma tilasta mata komawa addinin Kirista.
Tun a wancan lokacin ne dai DSS ta maƙale kan kujerar naƙi duk da umarnin da Kotun Majistiren ta bayar tana neman sakinta da kuma gurfanar da jami’in.
DSS ɗin ta ce ta nemi a soke umarnin kotun, tana mai cewa tana riƙe da Walida ne ƙarƙashin “kariya ta musamman”, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura a tsakanin jama’a da ƙungiyoyin farar hula.
Laifuka huɗu da ake zargin jami’in da aikatawa sun haɗar da sace yarinyar, yi mata fyaɗe, sabbaba kisan kai, tare da mayar da ita addinin kirista.
Yayin da yanke hukunci, Mai Shari’a Hassan Dikko na Babbar Kotun Tarayya, ya yi kakkausar suka kan yadda DSS ke gudanar da bincike kan jami’anta, yana mai cewa hakan ya saɓa wa tsarin doka.
Ya jaddada cewa binciken laifi nauyi da rataya a wuyan ‘yan sanda kacokam, kotu kuma ita ce ke da ikon yanke hukunci.
Kotun ta bayar da umarnin a saki yarinyar ba tare da wani sharaɗi ba, sannan ta umarci DSS ɗin da ta miƙa Onyewuenyi ga ‘yan sanda domin gudanar da cikakken bincike.
Masana shari’a sun ce hukuncin ya ƙara jaddada cewa babu wata hukuma da ta fi ƙarfin doka, tare da nuna muhimmancin raba iko tsakanin hukumomi.
Haka kuma, kotun ta yi watsi da binciken cikin gida da DSS ta gudanar, tana mai bayyana shi a matsayin yunƙurin kare jami’in daga ɗaukar alhaki.
Lauyan iyalan yarinyar, Kabiru Adamu, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga adalci da ke ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwar amincewa da ɓangaren shari’a.
A halin yanzu, hankali zai karkata kan ‘yan sanda domin ganin yadda za su gudanar da bincike, yayin da ake sa ran a tabbatar da gaskiya da adalci a shari’ar.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t