Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Bada Umarnin Ƙwace Kadarorin Ɗan Wani Dan Takarar Gwamna

Alfijr ta rawaito Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori da ke da alaka da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Neja, Liman Kantigi.

Hukumar Yaki da Hanci da Rashawa, EFCC, ta ce an bada umarnin ne bayan da kotu ta yi watsi da karar da Baba Chado Kantigi ya shigar na neman mallakar gida mai lamba 10, da ke kan titin Kinshasa, Wuse Zone 6 , Abuja a ranar Alhamis.

Chado-Kantigi ya shigar da karar ne domin neman mallakar kadarorin da ke da alaka da dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Liman Kantigi, tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu a jihar Neja a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Babangida Aliyu.

Mai shari’a Bature Gafai da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, ya yi watsi da karar tare da bayar da umarnin kwace kadarorin ga gwamnatin tarayya har abada.

Hukumar EFCC ce a shekarar 2017, ta kwace wasu kadarorin da ke da alaka da Kantigi bisa ga bayanan sirri da ke alakanta shi da karkatar da kudade da kuma kadarori.

Sanarwar ta kara da cewa “Wata kuma kadarar kasa mai alaka da Kantigi ita ce gida a Block 5, Flat 3, Divo Street, Foreign Affairs Quarters, Abuja”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *